Jamus za ta soma siyan gas daga Iraki
January 13, 2023Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya amince da soma cinikayyar iskar gas daga Iraki, an cimma wannan matsaya a yayin wata ziyara da ta kasance irinta ta farko da firaministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani ya kai birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus a wannan Jumma'a. A yayin ganawa da manema labarai, firaminista al-Sudani ya ce, kofarsu a bude take ga kamfanonin Jamus da ke son zuba jari da ma yin kasuwanci da kasar.
Kasashen biyu nada kyakyawar dangantaka a tsakaninsu, wanda ya sa a bara ma, a lokacin da kasar ke fama da matsalolin daga masu tayar da kayar baya, majalisar dokokin Jamus ta kada kuri'ar amincewa da tsawaita yawan sojojin kasar da ta tsugunar a Iraki har na tsawon shekara guda.