China na mamaye kasuwanni a kasashen Afirka | Siyasa | DW | 12.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

China na mamaye kasuwanni a kasashen Afirka

Manazarta na ganin cewar wannan yunkurin kasar China na kara kutsawa cikin kasashen Afirka wata babbar barazana ce ga kasashen Kungiyar EU da ma Amirka ta fuskar tattalin arziki.

Ministan harkokin waje na China Wang Yi ya kai wani rangadi a wannan sabuwar shekara a cikin wasu kasashen Afirka da suka hada da Madagaska da Tanzaniya da Zambiya da Kwango da Najeriya da nufin kara karfafa hulda ta kasuwanci da kuma dangantaka tsakanin kasashen. Manazarta na ganin cewar wannan yunkuri na kasar China na kara kutsawa cikin kasashen Afirka wata babbar barazana ce ga kasashen Kungiyar EU da Amirka ta fuskar tattalin arziki.

Babu wata nahiya ta duniya da China ta fi saka jari kamar nahiyar Afirka. A shekara ta 2016 China ta rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi na kasuwanci har 245 da kasashen Afirka wadanda za a iya kiyasta kamar kudade kimanin Dala biliyan 50 a karkashin wadannan kwangiloli kamar yadda wani kakakin ofishin ministan harkokin wajen na China ya bayyana, Wanda kuwa bisa ga dukkan alamu ya zarta irin jarin da Amirka ke zuba wa a Afirka da ma wasu sauran kasahen Turai wadanda suka yi wa kasahen na Afirka mulkin mallaka. Misali Zambiya na zaman cibiya ta harkokin sufiri da China ta ingata da kuma fanin noma da tattalin arziki. Kuma China ta kasance kawa ta farko ga kasashen na Afirka ta fuskar huldar tattalin arziki. Daga Habasha zuwa Djibouti China ta gina haryar layin dogo wanda yawancin kamfanonin kasar ne suka kaddamar da aikin yayin da ta kaddamar da tsare-tsare na tattalin arziki inda ta zuba jari biliyoyin daloli a Najeriya da Kenya ta hayar gina hanyoyi da madatsun ruwa da gadoji har zuwa fannin noma da kiwo. Angela Stanze Fellow wata masaniya a kan tsarin dokoki na nahiyar Turai:

''China na iya taimaka wa kasa ta fannin zuba jari har ma da sayar da makmai, ba ruwanta da ko ma wacce irin kasa ce da kuma irin tafarkin da take bi, duk da ma cewar wasu kasashen na Afirka na ammfani da ra'ayin kasashen Turai na tsari na demokaradiyya, ta ce hakan ya sa akwai babban hadari ga kasashen Kungiyar Tarrayar Turai da ma Amirka idan har China ta cigaba da kasancewa da karfi a Afirka.''

Bayan fafutukar da kasar ta China take yi a saka jari a nahiyar ta Afirka wasu muradunta da take kara kokarin kara dagewa a kai shi ne na ganin cewar ta tabattar da tsaro a nahiyar domin samun zaman lafiya domin kuwa bakwai daga cikin rundunonin kiyaye zaman lafiya na MDD cikin tara a Nahiyar Afirka dukkaninsu China ta kan bada  gudunmuwa, misali a Kudancin Sudan da Sudan da Mali da yankin Afirka ta Gabas da Djibouti ta aike da tawagar sojojinta.   Yayin da suma kasahen Amirka da Faransa ke da wasu sansanonin sojoji a wasu kasashen Afirka. abin da Stanze Fellow ta ce wani sabon salo ne.

''Salon na China na yanzu ya hada da sashen tsaro abin da ba a saba gani ba a baya domin neman jari kasar a shirye take ga sabbin tunani na yin hangen abin da ka iya zuwa ya zo a duniya idan har za ta samu riba.''

To sai dai duk da irin tasirin da China ke samu a nahiyar ta Afirka ana kuka da ita a game da irin  abubuwan da take wadanda ke da nasaba da take hakin ma'aikata da yin aiki da sinadarai marasa inganci da gurbata muhalli abin da kan shafi lafiyar al'umma kamar yadda Vince Chipatuka wata kwarara mai yin nazari a kan al'amuran tattalin arziki ta bayyana.

Sauti da bidiyo akan labarin