Cece- kuce a jam′iyyar PDP bayan da ta sha kaye | Siyasa | DW | 30.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece- kuce a jam'iyyar PDP bayan da ta sha kaye

Shugaban PDP Ahmad Adamu Mu'azu ya ki halartar waiwayen da jam'iyyar ta yi a kan musababbin shan kaye a zabukan da suka gudana, saboda barazanar tsigewa da ya ke fuskanta.

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi rahoton 'yan kwamitin yakin neman zabensa, a wani abun da ke zaman damar farko a tsakanin bangarorin PDP da har yanzu ke tunanin mafita ga makomar jam'iyyar. Sai dai kuma shi da ragowar manyan jiga- jigan jam'iyyar dai, ra'ayi ya zo kusan daya game da musabbabin asarar zaben da ke zaman irinsa na farko da kuma har ya zuwa yanzu ba su kai ga farfadowa a cikinta ba.

Sun yin intifakin cewa rikicin cikin gida da ma rashin hadin kan 'ya'yan PDP ne musabbabin da ya sa jam'iyyar asarar mukamai masu muhimanci ciki har da na shugaban kasa da kuma na gwamnoni a yayin zaben.

Nigeria Regierungspartei PDP

PDP na shirin zama jam'iyyar adawa a Najeriya

Sai dai kuma an kai ga mika rahoton ba tare da kasancewar shugabannin jam'iyyar na kasa baki daya ba musamman ma Ahmad Adamu Mu'azu da ke zama shugaban PDP. Tuni dai aka fara hasashen cewa gwamnonin PDP na kokarin tureshi daga shugabancin djam'iyyar tare da maye gurbinsa da Senata Liel Imoke gwamnan jihar Cross Rivers da ke shirin barin gado.

To sai dai kuma a fadar senator Walid Jibrin da ke zaman sakataren kwamitin amintattun PDP lokacin da jam'iyyar take ciki ba shi bukatar sabuwar baraka a tsakanin 'ya'yanta

Sauti da bidiyo akan labarin