1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga: Bayern Munich ta haye saman tebur

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
March 11, 2019

'Yan wasan Bayern Munich sun yi nasarar tumbuke Dortmund daga saman teburin Bundesliga.

https://p.dw.com/p/3EnOo
Bundesliga FC Bayern München v VfL Wolfsburg | Jubel
Hoto: Reuters/M. Dalder

'Yan wasan Bayern Munich sun yi nasarar harbin tsuntsaye biyu da dutse daya, inda a hannu daya suka karbe matsayin farko na Bundesliga a hannun Borussia Dortmund, yayin da Lewandowski ya zaba zama bako da ya fi zura kwallo a tarihin Bundesliga.

Wasannin mako na 25 na Bundesliga da suka gudana a karshen mako sun kasance masu matuar daukar hankali, kasancewa an yi karawa ne daga nesa tsakanin Dortmund da Bayern Munich da ke tafiya kafada da kafada da yawan maki. Sai dai Yaya Babba Munich ta yi amfani da wannan dama wajen nuna wa abokiyar hamayarta Dortmund cewa har yanzu ruwa bai kare wa dan kada ba, inda a gida Allianz Arena ta yi wa Wolfsburg dukan kawo wuka ci daya bayan daya har shida da nema. Wannan nasarar ta bai wa kungiyar da ta lashe kambun zakaran Jamus so shida a jere damar hayewa kan teburi da maki 57 sakamakon zarta Dortmund da ta yi da zura yawan kwallaye. Watanni biyar Bayern Munich ta shafe ta na kwan gaba kwan baya kafin yi nasarar dare wa saman teburi.

Duk da cewa ita Borussia Dortmund ta samu nasara a wasan da ta yi a Signal Iduna Park da Stuttgart da ci uku da daya, amma ta dandana kudarta kafin hakarta ta cimma ruwa.