Bundesliga: An janye izinin shiga filin wasa kallo | Labarai | DW | 10.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bundesliga: An janye izinin shiga filin wasa kallo

Za a ci gaba da mutunta dokar hana taron jama'a a Jamus har zuwa karshen watan Oktoba a wani mataki na hana yaduwar cutar Coronavirus da alamu ke nuni da cewa ba a shawo kan annobar ba.

Ministocin lafiya sun amince da a ci gaba da mutunta dokar hana taron jama'a har zuwa karshen watan Oktoban 2020, wannan na nufin ba za a bai wa 'yan kallon wasannin Bundesliga damar shiga filin wasanni kamar yadda aka amince a baya ba a yayin soma kakar wasan bana na daga ranar takwas ga watan Satumban bana.

Ministocin sun yanke shawarar ce a wannan Litinin, ganin yadda alkaluman masu kamuwa da cutar ke karuwa. Jami'an kiwon lafiya a na su bangaren, sun sha shawarta gwamnati kan yin takatsantsan a janye dokokin hana yaduwar cutar, sun nemi a ci gaba da daukar matakai na hana yaduwar cutar, da suka hada da sanya takunkumin rufe fuska da saka tazara a tsakanin jama'a.