Bukatar yin bincike kan kisa fararen hula a Abadam | Siyasa | DW | 19.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukatar yin bincike kan kisa fararen hula a Abadam

Kungyoyin kare hakkin dan Adama sun bukaci da a kiyaye rayukan fararen hular kana sun yi kira da a gagauta bincike kan harin jiragen saman yaki da suka yiwa wasu bayin allah kisan ba gaira

Kungiyoyin na Jamhuriyar Nijar sun yi wannan kiran ne a yayin da gwamnatin kasar ta Nijar, ta ce za ta binciki musabbabin harin, bayan ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku da ya fara a yau Alhamis.

A cikin wannan yanayi na juyayi gwamnati na nuna alhininta da ta'aziyarta ga iyallan mamatan da fatar lafiya ga wadanda suka jikkata, hakan kuma gwamnati za ta bude bincike sanin musabbabin harin tare da tantace ko wane jirgi ne ya kai farmakin, inji Marou Amadou, kakakin gwamnatin kasar ta Nijar.

Batun na ruwan bama-bamman dai a garin Abadam, na ci gaba da daukar hankali, ganin irin yanda har yanzu ko wace kasa ta kasa fitowa, domin daukar nauyin kai farmakin wanda yake a matsayin farmaki na farko mafi muni ga fararen hullar da basu san hawa basu san sabkaba. Inda birbishin yaki da Boko Haram ya farma su. Farfesa Jibrilla Abarshi, shugaban kungiyar ANDDH ne, wata kungiyar da ke kare hakkin dan Adam a Nijar.

Yace "Ina cike da mamakin abin da ya faru a garin Abadam, ganin cewar har yanzu ba wanda ya dauki nauyin kai farmakin. Duk kasar da ta aikata wannan ta san da ta aikata hakan, sai dai idan ta boye batun, domin jirgin yaki bai tashi ba tare da bashi umarnin inda za shi ba, kuma yakan je wurin da anka nuna mashi ya bada wuta. Kenan idan ya tashi da sanin hukumomin soja in ya tashi bisa ga umarnin da anka bashi ne"

Akalla mutun 37 ne suka rigamu gidan gaskiya, tare da jikkata wasu mutane sama da 20, wanda hakan ya haifar da dan ba a zukatan masu fafitakar kare hakkin dan Adam, tare da haifarda fargaba kan abinda kan iya faruwa a gaba.
Alhaji Moustapha Kadi, shi ne shugaban wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na CODDAE ya kuma bayyana cewa.

"Muna da fargaba domin idan har anka ci-gaba da hakan ba'a san wanda za'a kashewa ba, sabo da hakan za'a tarar da mutanen da basu ci basu sha ba a garinsu, suna biki ko addu'a, sai a sako masu bam. Wannan bai dace ba, domin yakin da muke yi da Boko Haram, muna yi ne don mu kare al'umma, ba wai don ita al'umma mu saka ta a cikin miyagun hali ba ne"

A cewar Malam Jibrilla Abarci malami a jami'ar Abdoul Moumouni dake Yamai, kuma shugaban kungiyar ANDDH, farmakin da jiragen suka kai, idan har cikin kuskure ne, to sun taka dokokin yaki "Su mutanen gari ne, basu cikin mayaka, in ba kuskure ba ne to bata yuwa akai musu hari sai kuskure, domin idan har cikin ganganci ne, to ya zamanto laifi a dokokin yaki, laifin kuma da ya kamata a hukumta".

Kafin wannan farmakin dai wasu masu sharhi na ganin tamkar an dan samu takon saka ne, tsakanin hukumomin tsaron Nijar da na Najeriya, inda ministan tsaron Nijar, ya yi subul da baka, ya ce sojansa ba irin na Najeriya da ke gudu bane, kalamun da kakakin sojan Najeriya, ya mayar masa da martani da kakkausar murya.

Wasu rahotannin da har yanzu ba'a tantance ba, na cewar al'ummar garin sun ga jirgin da ya yi farmakin na dauke da tutar Najeriya, abinda hukumomin kasar suka ce bincike ne kawai zai tantance hakan. A ko ina dai cikin kasar ta Nijar an sasauto da tutuci, domin girmama makokin da kasar ta ayyana, na kwanaki uku.


Sauti da bidiyo akan labarin