Bukatar inganta makamashi na bai daya a turai | Labarai | DW | 06.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar inganta makamashi na bai daya a turai

Sakamakon daukewan wutan lantarki da aka fuskanta a kasashen yammacin turai a karshen mako,Commissionan makamashi na kungiyar EU Andris Piebalgs,yayi kira dangane da bukatar kasashen kungiyar su samarda ingantaccen tsarin samarda makamashi na bai daya.Sanarwar daya gabatar ayayu na nuni dacewa,wannan matsala da aka fuskanta na bayyana yadda matsalar wani bangaren turan,ke shafar wasu,batu kuma dake bukatar ingantaccen tsarin inganta samarda da makamashi.Sakamakon karuwan bukatu na makamashi,adangane da shigowar yanayi na sanyi a nahiyar turai,ya kawo matsalar data haddasa daukewar wutan lantarki a wasu bangarorin Jamus da Faransa da Italiya da Spain,na tsawon mintuna 30,a ranar asabar da dare.Masanaantun makamashi a nahiyar turai dai na fadawa cikin irin wannan yanayi na karin bukatu,lokutan tsananin sanyi,kamar yanzu,ko kuma lokacin zafi,saboda karuwar amfani da injin na dumama daki.