Bukatar gyara a harkar zaben Najeriya | Labarai | DW | 14.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar gyara a harkar zaben Najeriya

Kungiyar da ta sanya idanu a zaben Najeriya na shekara ta 2015 da muke ciki daga Tarayyar Turai, ta nemi da a sake fasalin hukumar zaben kasar.

Jagoran sanya idanu a zaben Najeriya na kungiyar EU Santiago Fisas

Jagoran sanya idanu a zaben Najeriya na kungiyar EU Santiago Fisas

Kungiyar ta ce sake fasalin hukumar zai ba da dama ga jam'iyyu da ragowar masu ruwa da tsaki da harkokin zabe su taka rawa wajen nada shugaba da kwamishinonin hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC. Santiago Fisas da ya jagoranci kungiyar wajen sa ido yayin zaben dai ya ce duk da cewar zaben na cike da tarihin da babu kamarsa a shekaru 16 na sake dawowar demokaradiyya, akwai bukatar kari na matakai domin tabbatar da ingancinsa. Shawarwari dai-dai har 30 da suka hada da bada damar tsayawa takara karkashin independa da kuma hade tsarin tantancewa da kuma na zabe wuri guda da nufin rage bata lokaci. Ga batun yada labaran yakin neman zabe kuwa, sun nemi daukar mataki na ladabtarwa daga hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar, sakamakon abin da suka ce rashin dai-daito da kuma zargi ga kafafen yada labaran gwamnati na bada fifikon mai yawa ga jam'iyya mai mulki. Wakilinmu na Abuja Ubale Musa ya ruwaito cewa tuni Fisas ya mika sakamakon ga gwamnatin kasar da tai alkawarin yin nazarin shawarwarin.