Buhari zai fara ziyara a Nijar da Chadi | Labarai | DW | 03.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari zai fara ziyara a Nijar da Chadi

Makasudin ziyarar Muhammadu Buhari a Nijar da Chadi na zama tattaunawa kan hanyoyin da shugabannin kasashen za su bi wajen murkushe 'yan Boko Haram.

Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari shugaban Najeriya

A ranar Laraba ne shugaba Muhammad Buhari na Najeriya ke ziyara ta farko tun bayan kama mulkinsa a ranar Jumma'a da ta gabata, inda zai ziyarci makwabciyar kasar ta Najeriya wato Jamhuriyar Nijar, ziyarar da ake ganin babban makasudinta ke zama tattaunawa kan hanyoyin da shugabannin kasashen za su bi wajen murkushe 'yan ta'addar Boko Haram.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da a yau kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International za ta bayyana sabon rahoto kan zargin sojojin kasar da ayyukan take hakkin bil' Adama a lokacin da suke yaki da Boko Haram.

Ko da a cikin jawabin shugaban kasar ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda a kasar, su suka hallaka tsohon shugaban kungiyar ta Boko Haram Muhammad Yusuf , kalaman da ake wa kallon za su bude sabon babi a batutuwa da suka shafi take hakkin bil'Adama a wannan kasa da suka yi sanadin kunna rikicin da kasar ta samu kanta a ciki yanzu haka.