Boko Haram za ta sako matan Chibok 83 | Labarai | DW | 16.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram za ta sako matan Chibok 83

Fadar shugaban Najeriya ta ce kungiyar Boko Haram ta amince ta saki 83 daga cikin 'yan matan nan Chibok da suka sace shekaru biyun da suka gabata bayan da a 'yan kwanakin da suka gabata suka saki 'yan mata 21.

Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bangaren kungiyar da ke rike da 'yan matan ya bayyana cewar a shirye ya ke ya saki 'yan matan in har za a zauna kan teburin tattaunawa da shi. Kakakin na gwamnatin Najeriya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar shi wannan bangare wanda Musab al-Barnawi ke shugabanta ya ce sauran 'yan matan na hannun daya bangaren kungiyar ta Boko Haram wanda Abubakar Shekau ke jagoranta.