Boko Haram ta sako ′yan matan Chibok 21 | Labarai | DW | 13.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta sako 'yan matan Chibok 21

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da cewa Kungiyar Boko Haram ta sako 21 daga cikin 'yan matan sikandren Chibok da kungiyar ta sace sama da shekaru biyu da suka gabata. 

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da cewa Kungiyar Boko Haram ta sako 21 daga cikin 'yan matan sikandren Chibok da kungiyar ta sace sama da shekaru biyu da suka gabata. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa wata majiya ta yankin Banki na kan iyaka da kasar kamaru ta kwarmata masa cewa an yi musayar 'yan mata ne a yau da safe a yankin da wasu mayakan Boko Haram guda hudu da ake tsare da su. 

Kuma an kai 'yan matan ne a kauyen Kumshe da ke a nisan kilomita 15 da garin na Banki da misalin karfe uku na dare, a yayin da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram su hudu aka dauko su daga birnin maiduguri a cikin jirgin soja mai dirar angulu zuwa garin na Banki inda daga nan ne aka tafi da su cikin wata motar hukumar agaji ta kasa da kasa ta Redikuros zuwa kauyen na Kumshe inda a nan ne aka gudanar da musayar. 

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu Kakakin shugaba Muhamadu Buhari ya fitar ya ce an sako 'yan mata 21 a karkashin jagorancin Kungiyar ta Redikuros ta kasa da kasa wato CICR da kuma gwamnatin kasar Switzerland. Sai dai bai kawo zance cewa an yi musanyar 'yan mata ba ne da wasu 'ya'yan Kungiyar ta Boko Haram da ke a tsare. 

 

Sauti da bidiyo akan labarin