Boko Haram ta halaka fararan hula 88 a Nijar | Labarai | DW | 04.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta halaka fararan hula 88 a Nijar

MDD ta ce Boko Haram ta kashe fararan hula 88 ta kuma tilasta wa mutane dubu 18 barin gidajensu a yankin Diffa na Kudu maso gabashin kasar a cikin watan Maris din da ya gabata kadai.

MDD ta bayyana damuwarta dangane da halin da ake ciki a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar inda ta ce kungiyar Boko Haram ta halaka fararan hula 88 a watan Maris kadai a yankin Kudu maso Gabashin jamhuriyar Nijar a cikin jerin hare-haren da kungiyar ta zafafa wadanda kuma suka cilasta wa mutane sama da dubu 18 tserewa daga garuruwansu zuwa Diffa babban birnin yankin da wasu manyan kauyika na yankin.

 A cewa Kungiyar kula da ayyukan jin kai ta MDD Ocha reshen birnin Yamai, kungiyar ta Boko Haram ta kai hare-hare 21 kan fararan hula da sojoji tare da kona gidaje kimanin 100 da yin awon gaba da mata masu yawa a yankin a cikin tsukin watan na Maris kadai. 

Kungiyar ta kara da cewa yanzu haka mutanen da suka bar garuruwan nasu na ci gaba da kwararowa tara da tarewa a sansanoni dabam-dabam a yankin na Diffa. Lamarin da ta ce na kara haifar da barazanar tsaro a yankin na Diffa na yankin Tafkin Chadi