Kamar yadda suka saba kowace shekara a daidai wanan lokaci na watan hudu, Gobirawan masarautar Tsibirin Gobir da ke cikin jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da shagulgulan bikin sallar budin daji. Wannan biki na zaman guda cikin al'adun gargajiya da masarautar Gobir ke alfari da su saboda matsayi da dogon tahirin da yake dauke da shi cikin duniyar al'adun gargajiya.