Ba bu wani ci gaba game da matsalar bashin kasar Girka | Labarai | DW | 22.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba bu wani ci gaba game da matsalar bashin kasar Girka

Hukumomin lamuni na duniya da gwamnatin birnin Athens na kokarin cimma matsaya game da matalsar bashin kasar Girka.

Sai dai fatan samun wata maslaha na kara gushewa, gabanin wani taron koli na musamman da shugabannin kasashen Turai masu amfani da kudin bai-daya Euro za su yi da yammacin wannan Litinin a Brussles. Da rana an kammala wani taron ministocin ministocin kudi na kasashen kudin bai-daya na Euro ba tare da cimma wani sakamako ba. Taron dai ya kamata ya shirya taron kolin shugabannin. Wolfgang Schäuble shi ne ministan kudin Jamus ya yi karin haske.

Ya ce: "Kawo yanzu ba mu samu wasu shawarwari masu gamsarwa ba da za su zama madogara ga abin da ya kamata kungiyar kasashe masu amfani da kudin Euro su yi wato shirya wa taron kolin shugabannin Euro. Ba a samu wani canji ba tun ranar Alhamis da ta gabata."