Ba a rabu da Bukar ba a kasar Burundi
May 14, 2015Talla
Tsohon shugaban hukumar leken asirin Burundi Janar Godefroid Niyombare ya yi yunkurin hambarar da Pierre Nkurunziza daga gadon mulki. Sai dai rundunar tsaron kasar ta ce wannan yunkurin ya ci tura.Lamarin da ya haddasa wani sabon rikici tsakanin masu goyon bayan tazarcen shugaban kasa da kuma masu adawa da wannan mataki saboda a cewarsu ya sabawa doka.