Rikicin Burundi ya sa al'umma tserewa
April 16, 2015Talla
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bayyana damuwarsa dangane da rahotannin tashe-tashen hankulan da ake samu daga Burundi gab da za a yi zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga jagororin kasar da su tabbatar an yi zabe mai tsabta.
Batun cewa mai yiwuwa shugaba Pierre Nkurunziza ya nemi wa'adi na uku - duk da cewa bai riga ya bayyana wannan kudurin a hukumance ba- ya janyo rikicin da ake kwatantawa a matsayin mafi muni tun bayan yakin basasar kasar na shekaru 12, wanda aka gama a shekara ta 2005. Yanzu da dai 'yan kasar da dama sun tsere zuwa makwabciyarsu Ruwanda domin samun mafaka