Badakalar siyasa a Burundi | Labarai | DW | 02.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badakalar siyasa a Burundi

Gwamnatin kasar Burundi ta sha alwashin yin amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da shirin tazarce na Shugaban Pierre Nkurunziza.

Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi

Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi

Gwamnatin dai na zargin 'yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula da suka shirya wannan zanga-zanga da yin hanya ga wadanda ta kira da 'yan ta'adda da suka kai wani hari kan jami'an 'yan sandan kasar da gurneti, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar muitane uku ciki kuwa har da jami'an 'yan sandan biyu.

Ministan tsaron kasar Janar Gabriel Nizigama ya bayyana hakan inda ya zargi wadanda suka shirya zanga-zangar na da hannu a harin da aka kai din.