Masu adawa da Nkurinziza na ci gaba da bore | Labarai | DW | 04.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu adawa da Nkurinziza na ci gaba da bore

Bayan tsagaitawa na yini biyu, 'yan adawa da tazarce a karo na uku na shugaban kasar Burundi sun sake bazama a kan tituna domin ci gaba da bore.

Wasu masu gangamin sun cimma isa babban birnin kasar ta Bujumbura, inda a baya suka kasa isa saboda sojoji da 'Yan sanda da aka jibge. Ana iya jin karar harbin bindiga, mutane kuma na kokarin gudu, a yayinda masu shaguna ke rufewa.

Sojoji dai na cigaba da nuna halin "yaya babba" tsakanin masu zanga-zangar da jami'an 'yansanda, wadanda a wasu lokuta aka zarga da amfani da harsashi akan mutane. 'Yan sandan dai sun yi ta harbawa jama'a hayaki mai sa hawaye.

Kungiyar bada agajin kasa da kasa ta Burundi da shaidar da cewar, a kalla mutane shida suka rasa rayukansu a rikicin daya barke tsakanin 'yan sanda da masu boren adawan.