Kokarin murkushe masu adawa da tazarce a Burundi
April 27, 2015Talla
Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka kwace lasisin izinin aiki na wannan gidan Radiyo inda a gefe guda kuma hukumomin suka soma farautar wasu shugabannin kungiyoyin farar hula. An dai cafke shugaban hadaddiyar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Pierre-Claver Nmbonimpa tare da bada sammacin kamo Vital Nshimirimana jagoran kungiyoyin farar hula bisa kaddamar da wani kampe na nuna adawa ga shugaba Nkurinziza. Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kimanin 'yan kasar ta Burundi 15,000 ne suka tsere zuwa makwabciyarta Ruwanda domin tsira da rayukansu daga barazanar kisa da kungiyar 'yan bangar siyasa ta Nmbonerakure da ke goyan bayan tazarcen na Shugaba Nkurinziza ke yi musu.