Azumi cikin rashin kudi da tsadar rayuwa | Siyasa | DW | 06.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Azumi cikin rashin kudi da tsadar rayuwa

A Najeriya da Nijar al'ummomin ƙasashen sun soma gudanar da azumin watan Ramadan cikin wani hali na tsadar rayuwa sakamakon yadda frashin dan abin masarufi ya tashi a bisa kasuwanni.

Bayan da a yau aka ɗauki azumin watan Ramadan a yankin kudu maso yammacin na Najkeriya al'umma na kokawa da rashin kudi a birnin Lagas na Najeriya inda wakilinmu ya tabbatar da cewar frashin kayan abinci ya tashi a dalilin azumin.

Rayuwa al'umma a cikin watan azumi mai tsarki

Watan na azumin na Ramadan wanda ke zaman na ibada mafi girma ta addinin musulunci ya zo ne cikin wani hali da jama'a a Najeriya ke kokawa da rashin kuɗi, sakamakon yadda tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare.A lokutan gudanar da bikin Kirsimeti a wasu wurare a kan sami rangwame na kayan farashin masarufi amma a yanzu a lokacin ibadar mabiya addinin musulunci da wuya a sami rangwame na farashin duk kuwa da matakan da shugabannin addini ke ɗauka na samun sauƙin lamarin.

A Nijar shugabanni na yin kira ga 'yan kasuwa da su yi rangwame

A ranar farko ta kama azumin sarakunan gargajiya gami da hukumom sun yin kira ga 'yan kasuwar da su yi rangwame na kayan abinci, saboda darajar wannan wata mai alfarma.Haka ma shugabannin addiniai sun yi kira ga 'yan kasuwar da su yi sassauci.A birnin Zinder da ke a gabashin Nijar hukumomi sun gargaɗi 'yan kasuwar da su karya frashin kayan abinci saboda watan mai alfarma.

Sauti da bidiyo akan labarin