Austriya ta tsawatarwa Girka kan ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 03.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Austriya ta tsawatarwa Girka kan 'yan gudun hijira

Ministan harkokin wajen Austriya ya bukaci kasar Girka data takawa ‘yan gudun hijira birki da ke cigaba da yin tattaki zuwa arewacin Turai.

Ministan ya ce akwai bukatar mahukuntan Girkan dakatawa da yiwa sabbin masu neman mafakar rijista a sansanonin da aka kebe.

Sebastian Kurz a yayin da yake zantawa da mujallar Sueddeutsche Zeitung ta Jamus yayi nuni da cewar akwai bukatar kawo karshen munufar Girka wajen haramtawa masu gudun hijirar tsallakowa turai, a inda ya kara da cewar wadanda suka samu suka tsallako zuwa Girka a iya barin su.

Yanzu haka dai mashiga biyu ce 'yan gudun hijirar ke amfani dasu wajen tsallakowa da suka hada da kasashen Girka da Italiya domin bazamowa cikin kasashen turai, a inda kasashen ke cigaba da samun suka daga takwarorin su na turai kan rashin tabuga komai wajen dakile kwararar 'yan gudun hijiran zuwa turan.