Atiku Abubakar ya sake komawa PDP | Labarai | DW | 04.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Atiku Abubakar ya sake komawa PDP

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya sake komawa jam'iyyar PDP mai adawa a kasar abin da ke nuna cewa ya sake damara ta neman shugabancin na Najeriya a shekarar 2019.

Atiku Abubakar dai ya yi wani bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya ce ya sake komawa jam'iyyar ta PDP saboda gazawar jam'iyyar APC mai mulki wajen cika alkawuran da ta yi wa al'ummar Najeriya tun bayan da ta hau kan karagar mulki a shekarar 2015.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Atikun ke sauya sheka, ya bar PDP ya yi takara a ACP a 2014 a lokacin ya ce jam'iyyar ta PDP ta gaza. Ya dai nemi shugabancin na Najeriya karkashin jam'iyyu uku idan aka koma tarihi tun daga shekarar 1993.