Asusun Taimakon Yara na Majalisar Dinkin Duniya | Amsoshin takardunku | DW | 17.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Asusun Taimakon Yara na Majalisar Dinkin Duniya

Takaitaccen bayanin Asusun Taimakon Yara na Majalisar Dinkin Duniya

Jami'an unicef

Jami'an unicef

Masu sauraronmu barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hanun mai sauraron mu a yau da kulum Abdullahi Bello Uban Dawaki mazauni a karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto a tarayar Nigeria,mai sauraron namu cewa yayi dalilin rubuto muku wanan wasika shine,don Allah ku yi min karin bayani kan hukumar nan mai kula da kanan yara ta majalisar dikin duniya wato(UNICEF)shin daga inna hukumar take samun makudan kudaden da take kashewa wajen gudanar da aiyukanta,saboda naga magungunan da take baiwa yaran Africa kyautane,inda yace abin na daure masa kai.

Ko shin kasahen Africa ne kawai ke fama da ciwon shan inna wato Polio,su kasahen turawa basu da wanan cuta ne.

Amsa—Asusun dai na talafawa kanan yara na majalisar dinkin duniya da aka fi sanni da Unicef an kafa shine a shekara ta 1946,don bada taimako ga kanan yaran da hadarin yakin duniya na biyu ya ritsa da su.Tun shekara ta 1953 ne asusun tallafawa kananan yaran na majalisar dikin duniya ya fadadda aiyukansa ga kasashe masu tasowa,inda hukumar ta Unicef ta rika sanya baki kan al’amuran da suka shafi hakkin kananan yara da nufin bada kariya a wannan fuska.

Wannan hukuma dai ta Unicef dake lura da tallafawa kanananan yara na zaman hukuma daya tilo data damu da biyan bukatun kanan yara.

Banda ma tallafawa kanan yara asusun na kula da kananan yara na majalisar dikin duniya na Unicef,na gabatar da manufofi na bada taimako a fannin ilimi da kuma kula da lafiyar kanan yara a duniya baki daya.

Asusun dai na tallafawa kananan yara na majalisar dikin duniya ya gudanar da aiyuka na jin kai ga kananan yara a kasahen Africa inda aka fi fama da matsaloli na yakin basasa kamar dai yadda lamarin yake a kasahen Saliyo,Liberia,jamhuriyar demordiyar Congo, yankin Darfur na kasar Sudan da dai sauran su.

Inda kuma ana magana game da inda hukumar ta Unicef ke samun kudaden da take tafiyar da aiyukanta,sai mu ce ta na samun tallafi ne na irin kasafin da majalisar dikin duniya ke ware mata duk shekara.da kuma irin taimakon da ake samu daga kasashe masu tagomashin tattalin arziki.

A kuma game da cewar ko a nahiyar Africa ne aka fi fama da ciwon shan inna wato Polio,sai mu ce a kasashen tuwara akwai kananan yaran dake fama da cutar shan inna,sai dai irin matakan da suke dauka na yaki da wannan cuta a kasashen su ya sha baban da yadda lamarin yake a kasahe masu tasowa na Africa.Kai banda cutar Polio akwai ma mutanen dake fama da cutar kuturta da sauran cututtuka kamar yadda muke da mutane masu fama da irin wanan cututtuka a rukunin kasahe masu tasowa.

Dafatan mai sauraron namu ya gamsu.

 • Kwanan wata 17.10.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BwXK
 • Kwanan wata 17.10.2005
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BwXK