Asusu na musamma na Majalisar Dinkin Duniya don kai daukin gaggawa | Labarai | DW | 16.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asusu na musamma na Majalisar Dinkin Duniya don kai daukin gaggawa

Babbar mashawartar MDD ta amince da ware kudi Euro miliyan 420 ga wani asusu na musamman, don ba da taimakon gaggawa ga wuraren da bala´o´i daga Indallahi wato kamar girgizar kasa ko mahaukaciyar iska suka afkawa. Babban sakataren MDD Kofi Annan ya ce wannan asusun zai ba majalisar sukunin daukar matakan gaggawa ba tare da ta jira wani taimakon kudi don kai dauki ga wuraren da bala´i ya afkawa ba. Annan ya ce kawo yanzu asusu na musamman da majalisar ke da shi mai kasafin kudi euro miliyan 50 yayi kadan wajen tafiyar da wannan aiki na taimakon gaggawa.