Assad ya goyi bayan tsagaita wuta a Siriya | Labarai | DW | 02.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Assad ya goyi bayan tsagaita wuta a Siriya

Shugaban Siriya ya nuna goyon bayansa ga shirin tsagaita wuta da kasashen duniya suka taimaka aka kulla tsakanin bangarori daban-daban a kasar.

Shugaba Bashar al-Assad na Siriyan ya bayyana goyon bayansa kan shirin tsagaita wutar da aka fara aiki da shi tun ranar Asabar din da ta gabata tsakanin bangarorin da ke rikici na kasar.

Assad ya shaida wa tashar talabijin ta Jamus ta ARD a hirar da suka yi da shi cewa mayaka na bangaren adawa suna iya koma rayuwa kamar yadda aka saba idan suka mika makamai.

Kasashen Rasha da Amirka ne dai suka jagoranci kulla yarjejeniyar tsagaita wutar ta Siriya tsakanin kungiyoyi kusan 100 masu dauke da makamai. Sai dai yarjejeniyar ba ta kunshi kungiyoyi biyu ba na IS da ke neman kafa daular Islama da kuma Nusra mai nasaba da al-Qaeda, wadanda ake ci gaba da musu barin wuta.