1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta hukunta mutane 5 saboda leken asiri

Zainab Mohammed Abubakar
August 11, 2020

Mahukuntan Iran sun capke 'yan kasar guda biyar saboda zarginsu da leken asiri wa kasashen Izra'ila da Birtaniya da kuma Jamus, tare da zartar da hukunci a kan biyu daga cikinsu.

https://p.dw.com/p/3goda
Iran Justiz-Sprecher Gholamhossein Esmaili
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Ataei

Da yake jawabi wa manema labaru, kakakin sashin shari'ar Gholamhossein Esmaili ya gabatar da Shahram Shirkhani a matsayin sunan daya daga cikin mutane biyar da ake tuhumar, wanda a cewarsa yana leken asiri wa Birtaniya.

Ya kara da cewar tuni Shirkhani ya bayar da bayanan kasa masu muhimmanci da suka hadar da na hada-hadar bankuna da kwangiloli a ma'aikatar tsaro, wanda tuni aka yanke masa hukuncin zama gidan kaso.

An zartar da hukuncin daurin shekaru 10 wa Masoud Masaheb, daya daga cikin shugabannin kamfanin hadin gwiwa Iran da Austriya mai suna Friendship Society, saboda samunshi da laifin musayar bayanan sirri da hukumomin leken asirin Izra'ila da Jamus, kan shirin makaman nukiliyar Tehran.