Ana taro kan kawo karshen cutar Ebola | Labarai | DW | 03.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana taro kan kawo karshen cutar Ebola

Shugabannin kasashen Laberiya, da Guinea, da kuma Saliyo na halartar taro kan neman kawo karshen cutar Ebola.

Shugabannin kasashen yankin yammacin Afirka da cutar Ebola ta yi wa illa sun nemi karin taimako domin kawar da cutar da sake bunkasa tattalin arziki. Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kasar Laberiya, da Shugaba Ernest Bai Koroma na Saliyo, da kuma Shugaba Alpha Conde na kasar Guinea suna cikin masu halartar babban taron kan kawar da cutar ta Ebola da ke gudana a birnin Brussels na kasar Belgium.

Kusan mutane 10,000 cutar ta hallaka daga cikin mutane 24,00 da suka kamu, tun lokacin da aka gano barkewar cutar ta Ebola a yankin kudancin kasar Guinea a watan Disamba na shekara ta 2013. Ana bukatar kimanin taimakon dala milyan dubu-dari-hudu da rabi domin tunkarar chutar ta Ebola, sai dai rabi adadi ne aka samu.