Ana kai ruwa rana kan Sweden da Finland | Siyasa | DW | 30.06.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana kai ruwa rana kan Sweden da Finland

Ukraine ta samu gagarumar goyon baya da tallafin kudade a yayin da Turkiyya ke barazanar hawa kujerar na ki kan shigar da Sweden da Finland a cikin kawancen NATO.

Yini biyu kacal da cimma matsaya na kawar da duk wata adawa da shigar da Sweden da Finland cikin kungiyar tsaro ta NATO, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadin cewar, Ankara na iya hawan kujerar na ki, idan har kasashen ba su cika ka'idojin da aka gindaya musu ba.

Spanien Nato-Gipfel in Madrid - Präsident Recep Tayyip Erdogan

Shugaban Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya

Shugaba Erdogan ya ce, zai iya kin amincewa da shigarsu NATO, idan har suka gaza cika sabuwar yarjejeniyarsu da Turkiyya. Erdogan ya yi wannan gargadi ne a karshen taron yini biyu na kungiyar tsaron da Amirka ke wa jagoranci, ta gayyaci kasashen biyu don su hade a wannan hadaka mai wakilan kasashen 30 a hukumance.

Game da halin da ake ciki a yakin Ukraine kuwa, shugaban na Turkiyya ya jaddada muhimmancin daukar matakan da suka wajaba na gano bakin zaren warware rikicin da ke ci gaba da ta'azzara. Ya ce " Dole ne mu kawo karshen wannan yanayi da al'umma ke ciki na asara da zubar da hawaye cikin gaggawa. Mu kara karfafa kokari na diflomasiyya domin cimma tsagaita wuta na dindindin".

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a na shi bangaren, farin ciki ya nuna dangane da matakin da aka kai na amincewa da kasashen Sweden da Finland zuwa cikin kawancen tsaron na NATO. Ya ce" Kungiyar ta yanke shawara mai muhimmanci a tarihi a yayin wannan taron kolin na karbar sabbin mambobi biyu, Finland da Sweden. Dukansu kasashen biyu za su sami dawwamammen karfafa  kawancenmu, ta fuskar soji da kuma ta siyasa."

Spanien | NATO Gipfel in Madrid Joe Biden

Biden zai ba wa Ukraine taimakon dala miliyan 800

Shugaba Joe Biden ya ayyana cewar,  Amirka za ta bada karin tallafin makamai da wasu kayan soji na wajen dala miliyan 800 wa Ukraine, tare da yabawa bajintar al'ummar kasar tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar a karshen watan Febrairu.
Jagoran kawancen kungiyar tsaron, Jens Stoltenberg ya ce, za su karfafa goyon bayansu wa kasashen nahiyar Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da kungiyar NATOn ke la'akari kalubalantar tasirin da Rasha da Chaina ke kara yi a yankunan.

A yayin taron birnin Madrid na kasar Spain, shugabannin kawancen na NATO sun yi muhawara kan yadda kasashen Rasha da Chaina ke ci gaba da yin tasiri a harkokin siyasa da tattali da soji a wadannan yankunan na kudanci.  A kan haka ne, Stoltenberg ya ce, kungiyar ta amince da samar da shiri na kariya, domin taimaka wa kasar Mauritaniya kare kan iyakokinta daga ayyukan ta'addanci, tare da karin tallafi ga kasashen Jordan da Tunisiya.

Wakilan kasashen na NATO da ke yankin kudanci, ciki har da mai masaukin bakin taron na yini biyu wato Spain, sun bukaci kungiyar ta kara mayar da hankali dangane da barazana da ke fitowa daga Afirka. Madrid na kara bayyana damuwa a dangane da bakin haure da ke amfani da kasar a matsayin mashigin shiga nahiyar Turai.

Sauti da bidiyo akan labarin