NATO za ta agaza wa Ukraine idan ta kama | Labarai | DW | 29.06.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO za ta agaza wa Ukraine idan ta kama

NATO ta sha alwashin taimaka wa Ukraine muddin ya cancanta a fuskar mamayar Rasha. Kungiyar ta bayyana haka ne a yayin wani taron koli a birnin Madrid na Spain.

Kungiyar tsaron ta NATO ta yi gargadin cewar za ta iya taimaka wa Ukraine idan har hakan ya cancanta, a nan gaba lokacin da kasar ta shiga cikin kungiyar EU. A halin da ake ciki Ukraine  ta ce ta yi musayar sojoji fursunoni 144 da Rasha, ciki har da masu kare Azovstal 95 a Mariupol da ke kudu maso gabashin kasar, wadanda suka yi yaki a tashar jiragen ruwa da sojojin Rasha suka yi wa kawanya tsawon makonni kafin su mika wuya. Yawancin fursunonin da aka yi musayarsu sun ji munanan raunuka harsassai a cewar hukumomin na Ukraine. Kyiv da Moscow sun gudanar da musayar fursunoni da dama tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.