1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO: Burin kasashen Filland da Sweden

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 29, 2022

Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, ba su cimma matsaya ba a tattaunawarsu da wakilan kasashen Filland da Sweden da ke son shiga kungiyar tsaro ta NATO.

https://p.dw.com/p/4C0ij
Turkiyya I Ankara | Shugaba Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHoto: Murat Kula/AA/picture alliance

Shugaba Racep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, tattaunawar tasu ta makon da ya gabata ba ta cimma fatan da ake da shi ba. A cewar Erdogan Ankara ba za ta goyawa kasashen da take zargi da marawa 'yan ta'adda baya su shiga cikin kungiyar tsaron ta NATO ba, kamar yadda kafar yada labaran kasar TRT ta ruwaito. Turkiyya dai ta yi watsi da bukatar kasashen na Filland da Sweden din ta shiga NATO, inda aka ruwaito Erdogan na cewa ba su da gaskiya a wata hira da ya yi da manema labarai bayan dawowarsa daga wata ziyarar aiki da ya kai Azerbaijan.