1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar NATO ta kara taimakon Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar LMJ)(SB
March 24, 2022

Shugabannin manyan kasashen duniya na kungiyar tsaron NATO masu fada aji, sun saurari koken shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy na bukatar karin tallafin kayan sojoji domin kare mutanensa daga hare-haren sojojin Rasha.

https://p.dw.com/p/490Dj
Beljiyam | Taron kungiyar tsaron Nato kan rikicin Ukraine
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa (hagu) da Olaf Scholz Shugaban Gwamnatin Jamus (dama)Hoto: Markus Schreiber/AP Photo/picture alliance

Taron da ke gudana karkashin jagorancin kungiyar tsaro ta NATO/OTAN da ta kasashe masu mafi karfin tattalin arziki ta G7 da kungiyar Tarayyar Turai, EU, ya nuna fargaba dangane da abin da suka kira "rashin hangen lokacin da wannan rikici zai kare", kuma ka iya yaduwa zuwa wasu kasasahe.

A yayin da Turai ke cikin barazanar fadawa matsala mafi girma na tsawon lokaci, kasasahen Yammacin Duniya na ci gaba da laluben hanyoyin kara matsin lamba wa shugaba Vladimir Putin na Rasha, tare da kauce wa matakan da za su iya kara ta'azzara fada ya yadu zuwa wasu yankunan nahiyar. Amirka dai ta sanar da karin takunkumi a kan Rasha da kayan agaji ga al'ummar Ukraine.

Beljiyam | Taron kungiyar tsaron Nato kan rikicin Ukraine
shugabannin kasashen kungiyar NATOHoto: Eric Lalmand/BELGA/dpa/picture alliance

Shugaba Joe Biden na Amirka da ya halarci taron na Brussels ya sake jaddada matsayinsa na mara wa Ukraine baya. Sai dai Kungiyar kawance tsaro ta NATO a daya bangaren ta ce, ba za ta amsa kiran da mahukuntan birnin Kiev ke yi na bukatar kafa dokar hana shawagin jiragen sama ba, balle tura sojojin kawancen, kamar yadda babban jami'inta Jens Stoltenber ya jaddada.

A jawabinsa ga mahalarta taron ta yanar gizo, Shugaba Volodymyr Zelenskyy  kamar yadda ya saba, ya roki kasashen Yamma da su agaza masa a fannin kayan yaki marasa adadi, saboda Rasha tana kai hare-hare mara iyaka a Ukraine. Ya nemi da su ba shi makaman kariya ta sama da ta cikin ruwa. Sai dai duk da godiyar da ya yi musu saboda irin tallafa masa da suke yi, shugaban na Ukraine ya kasa boye takaicinsa.