1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fuskantar tarnaki kan yakin neman zaben Tinubu

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
October 13, 2022

A Najeriya tsugune ba ta kare ba a jam'iyyar APC mai mulki a game da mutanen da za su jagoranci yakin neman zaben dan takarar neman shugabancin kasar Bola Ahmed Tinubu.

https://p.dw.com/p/4I9vW
Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a Najeriya
Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a NajeriyaHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Matsala ta sake fitowa fili ne a wani taro da gwamnoninta da wani kwamitin jam'iyyar suka yi, wanda ya waste ba tare da cimma wata matsaya ba a kan batun wadanda za su jagoranci tallata Tinubun, abin da ya sanya jam'iyyar gaza kaddamar da yakin neman zabe aNajeriya.

Wannan zama da gwamnonin jam'iyyar ta APC suka yi a Abuja da sauran ‘yan kwamiti da ma bangaren wakilan yakin neman zaben dan takarar neman kujerar shugaban kasa a APC, na cikin tarba-tarbar da suke yi na nemo bakin zaren da har yanzu ya ki shiga kafar allura balle a yi dinki da shi, don dinke barakar da suke fuskanta a game da batun wadanda za su jagoranci yankin neman zaben da dankarar ya fitar.

Tun da farko dai jam'iyyar ce ta fara bara inda ta  nuna damuwa a kan mutanen da dan takararta Bola Ahmed Tinubu ya sanar da su a matsayin wadanda za su jagoranci takarar tasa.

Wannan takaddama dai ta sanya har ya zuwa wannan lokaci babu rana da ma lokacin da jam'iyyar za ta kaddamar da takarar. Sai dai shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu,  ya ce ana neman nuna masu gajin hakuri ne.

Hakuri ko gajin hakuri a harkar ta nuna a fili takaddamar da ake fuskanta a APCn a harkar yakin neman zaben shugaban kasa, da tun da farko ta fuskanci rarrabuwar kawunan wasu yayanta a game da fitar da dan takarar Musulmi kuma mataimakinsa ma Musulmi batun da har yanzu suke kokari na dinke barakar da hakan ya haifar.