An yi garkuwa da mutane tare da yi ma wasu kisan gilla a arewacin Najeriya | Labarai | DW | 18.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da mutane tare da yi ma wasu kisan gilla a arewacin Najeriya

Mutane 32 aka kashe sannan aka yi garkuwa da 185 a wani hari da Boko Haram ta kai kauyen Gumsuri da ke jihar Borno a ranar Lahadi da ta gabata.

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 32 sannan sun yi garkuwa da mutane 185 a wani hari da suka kai kauyen Gumsuri da ke jihar Borno a ranar Lahadi da ta gabata. Mazauna kauyen sun ce 'yan bindigan sun kona kauyen. Daga cikin wadanda aka sace akwai 'yan mata da yawa, inji wadanda suka tsira da ransu kuma yanzu haka suke birnin Maiduguri. Kauyen na Gumsuri dai bai da nisa da Chibok, inda a cikin watan Afrilu 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan makaranta fiye da 200. Daga Kamaru kuwa hukumomin kasar ne suka ce sojoji sun kashe 'yan bindigar Boko Haram 116 a wani gumurzu da suka yi kusa da kan iyaka da Najeriya.