1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza samun mafita kan nadin jiga-jigan EU

July 1, 2019

An dage taron shuwagabanni kungiyar Tarayyar Turai zuwa gobe Talata sakamakon gaza cimma matsaya gane da nadin kusoshin kungiyar.

https://p.dw.com/p/3LPvE
Belgien EU Gipfel in Brüssel - Angela Merkel
Hoto: Reuters/J. Geron


Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana fatan cimma matsaya game da nada jigajigan kungiyar Tarayyar Turai.  Wannan ya biyo bayan dage taron shugabanni kasashen Tarayyar Turan da ake gudanarwa a birnin Brussels na kasar Belgiyam izuwa Talata mai zuwa.

Tattaunawar ta yi tsauri a cewar Angela Merkel amma tana kyautata zaton  za a cimma matsaya idan duk bangarorin suka nuna sanin ya kamata.