An shiga rana ta biyu da sassauta dokar hana zirga-zirga a wasu jihohin Najeriya | BATUTUWA | DW | 05.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

An shiga rana ta biyu da sassauta dokar hana zirga-zirga a wasu jihohin Najeriya

Bayan sassauta dokar hana zirga-zirga da gwamnatin Najeriya ta yi a ranar Litinin da ta gabata a jihohin Legas da Ogun da kuma birnin Tarayyar kasar, mutane sun yi fatali da dokokin nesa da juna.

Wata sabuwar barazana ka iya kai wa ga kara ta'azarar annobar COVID-19 da ke  kara karuwa a Najeriya a halin yanzu, hukumomin kasar sun yi  barazanar sake  kulle manyan biranen Abuja da Legas da jihar Ogun in har aka ci gaba da ko'in kula da dokoki nesanta kai tsakanin al'umma.


An dai kai ga uwar watsi da sabbabin dokokin cudanyar sannan kuma aka koma tsohon tsari kama daga bankuna ya zuwa su kansu kasuwannin babban birnin tarrayar Abuja dama birnin Legas inda mazauna ke fatan samun damar biyan bukata a cikin wa'adin gwamnati. Abun kuma da ya kai ga su kansu hukumomin da ke jagorantar yakin barazanar sake mai da al'umma na biranen ya zuwa kulle  sakamakon al'adar da ke iya zama babbar barazana ga fashewar cutar a tsakanin al'umma.


Dr Chikwe Ihekwezu dai na zaman shugaban cibiyar kula da yaduwa ta cutuka ta kasa da kuma ya ce suna shirin sauyin taku in har ba a kai ga samun sauyin taku ba.

An dai shiga rana ta biyu tare da alamun sauyi, musamman  a bankuna da suka kara bude rassa sannan kuma suka sanya jami'an tsaro  da nufin cika umarnin nesanta kai tsakanin juna,  to sai dai kuma  a tunanin Dr Patrick Dakum da ke zaman wani likita a cibiyar kula da cutuka ta  Amurka a tarrayar Najeriya har yanzu da sauran tafiya a tsakani na mazauna birnin na Abuja da bin umarnin masanan lafiya da nufin kaucewa cutar

Mahukuntan birnin na Abuja dai sunce suna shirin nazarin nasara ta matakan na tsawon makonni biyun dake tafe , kafin yanke hukuncin karshe game da bukatar komawa cikin gidan ko kuma kara sassauta matakan a fadar .

Najeriya dai na tsakanin sassautawa a cikin matsin na lafiya da nufin inganta rayuwa, da kuma fuskantar barazanar barkewarta cikin kasar da tuni ke kukan rashin isassun kayan aiki.
 
 

Sauti da bidiyo akan labarin