An sako fasinjojin da aka yi garkuwa da su a Najeriya | Labarai | DW | 05.10.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako fasinjojin da aka yi garkuwa da su a Najeriya

'Yan bindgigar nan da suka yi garkuwa da gomman mutane cikin watan Maris a arewacin Najeriya, sun sako sauran wadanda ke a hannunsu, kamen da ya tayar da hankali a kasar.

A Najeriya an sako ilahirin mutanen da suka saura a hannun 'yan bindigar nan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a tsakanin Abuja da Kaduna, da aka kame tun cikin watan Maris na wannan shekarar.

Kwamishin watsa labaran gwamnatin jihar Kaduna a Najeriyar, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da sakin mutanen su 23 da suka saura a hannun 'yan bindigar Boko Haram.

Hukumomin kasar dai ba su ce komai kan yadda aka yi aka sako mutanen ba, musamman ma abin da ya shafi biyan kudin fansa.

Gungun 'yan bindiga ne dai suka bude wuta kan jirgin na kasa wanda ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kadunan cikin watan na Maris, suka kuma kashe wasu daga cikin fasinjoji sannan suka yi awon gaba da wasu da dama.

Kafin yau din dai, 'yan bindigar sun sake wasu da dama daga cikin fasinjojin.