1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi garkuwa da 'yan China a Najeriya

Abdul-raheem Hassan
June 30, 2022

Rahotanni daga Najeriya, na cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama tare da sace wasu 'yan kasar China hudu da wasu 'yan kasar a wani hari kan wata mahakar ma'adinai a jihar Niger da ke arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/4DTXT
Nigeriya  'yan sanda
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Jihar Niger na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke da gungun 'yan bindiga da ke addabar jama'a ta hanyar kisa da sace mutane domin neman kudin fansa.

Wani jami'in gwamnatin jihar ya shedawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, jami'an tsaro sun mayar da martani ga maharan a ranar Laraba, a Kauyen Ajata Aboki da ke gundumar Shiroro a Nijar.

Kawo yanzu ba a bayyana ko su waye suka kai hari kan mahakar ma'adinan ba tukuna, jami'an yankin sun ce a shekarar 2021, ana zargin Boko Haram sun kafa sansani a yankin Shiroro.