Jamus ta gargadi 'yan gudun hijirar Siriya
August 18, 2019Talla
Horst Seehofer, ya fadi hakan ne a yayin tattaunawa da jaridar kasar mai suna Bild am Sonntag, ya ce shawarci daukar matakin ne kan duk wani dan asalin kasar Siriya, da aka gano na yawan kai ziyara kasar bayan da ya nemi mafaka daga rikici. Ministan ya ce, muddun dan gudun hijira na iya kai da kawo wa a kasar, to ashe babu sauran barazanar da ya ke fuskanta, saboda haka dole Jamus ta dauki matakin janye takardar shedar zaman da ta bayar.
Yanzu haka ana sa ido kan rikicin na Siriya kuma da zarar an gamsu da wanzuwar tsaron kasar, za a soma mayar da 'yan gudun hijirar, inji ministan. 'Yan Siriya fiye da dubu dari bakwai ne suka tsere daga kasar zuwa Jamus, a tsawon shekaru takwas da yakin basasa ya barke.