An kammala zagaye na biyu na zaben ´yan majalisar dokokin Faransa | Labarai | DW | 17.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala zagaye na biyu na zaben ´yan majalisar dokokin Faransa

Dazu-dazunann aka rufe rumfunan zabe a Faransa inda a yau aka gudanar da zagaye na biyu na zaben ´yan majalisar dokokin kasar. Yanzu haka dai ana jiran sakamakon zaben wanda binciken jin ra´ayin jama´a yayi nuni da cewa jam´iyar UMP ta shugaban kasa Nicolas Sarkozy zata samu rinjayen kashi biyu cikin 3 a majalisar. Sarkozy wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar makonni 6 da suka wuce zai samu sukunin aiwatar da canje canje a fannonin haraji da kasuwar kwadago. Ita kuwa Segolene Royal wadda ta sha kashi a zaben shugaban kasa, ta yi kira ga magoya bayanta da su hana ´yan ra´ayin mazan jiya zama wuka da nama a harkokin siyasar kasar ta Faransa.