Hukumomin tsaro kasar Jamus na tsare da maharin tashar jirgin kasa tare da yin bincike kan dalilin tunkude yaron da jirgi ya markade a birnin Frankfurt.
Jami'an 'yan sandan kasar Jamus sun kama mutumin da ya tunkude yaro mai shekaru takwas a kan layin dogo a babbar tashar jiragen kasa da ke birnin Frankfurt, an kuma tabbatar da mutuwar yaron. Mahaifiyarshi da maharin ya so halakata ita ma, tana kwance a gadon asibiti. Wannan lamarin dai ya girgiza jami'an tsaron Jamus, inda tuni ministan cikin gida Horst Seehofer, ya yanke hutun da yake yi, ya dawo gida don ganawa da jami'an tsaro a kan lamarin.