An kai wa 'yan kasar Guinea hari a Jamus | Labarai | DW | 02.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai wa 'yan kasar Guinea hari a Jamus

A Jamus wasu mutane 'yan kasar Guinea su uku sun gamu da harin kyamar baki.

'Yan sanda sun ce sun samu bayanan da suka tabbatar musu cewa an kai wa wadannan mutane hari ne a saboda launin fatarsu, kuma daya daga cikin mutanen da abin ya shafa ya ji rauni sosai.

A halin da ake ciki mutane ukun suna asibiti inda suke jinya. Tuni dai 'yan sanda suka sanar da kamen mutane 12 bayan harin na ranar Asabar da ya gudana a wani fitaccen dandalin taruwar masu ra'ayin kyamar baki a birnin  Erfurt. Masu shigar da kara su ma sun ce sun fara bincike a kan lamarin domin kwato wa mutanen hakkinsu.