An fara jefa kuria a zaben yan majalisar Bahrain | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara jefa kuria a zaben yan majalisar Bahrain

An bude runfunan zabe yau a kasar Bahrain karamar kasa dake yankin gulf,cikin tasha tsahn hankula tsakanin gwamnati da yan adawa da suka janyewa zaben 2002.

A jiya jumaa ne dai babban jamiyar siyasa ta yan shia ta gargadi hukumomin kasar karkashin jagorancin yan sunni cewa,zata nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri nayin magudi cikin wannan zabe.

Mutane 295,000 suka cancanci jefa kuriarsu a zaben na yau,inda ake sa ran zasu zabe membobin majalisa 39 daga mazabu 39.

Yan takara 207 ne tsaya a wannan zabe cikinsu kuwa da mata 17.

Tuni dai wata mata Latifa al,Qouhoud ta samu nasarar dare nata kujerar saboda bata da abokin hamaiya a mazabarta,wanda hakan ya sanya itace mace ta farko yar majalisa a tarihin kasar Bahrain.