Kurdawa mazauna Jamus sun bukaci gwamnati ta dauki matakai kan masu akidar kyamar baki yayin da suke alhinin mutuwar mutane tara da dan bindiga ya harbe a wasu shagunan shan shiha a garin Hanau da ke tsakiyar kasar.
Tun a jiya Alhamis da balahirar ta afku Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier suka yi Allah wadai da muggan dabi'un, tare da jaddada aniyar hukuma na yaki da tashin hankali a fadin kasar a lokacin da suke zagayen jajantawa al'umma. To amma wani mai magana da yawun Kurdawan Ayten Kaplan mazaunin Gabashin Jamus ya bayyana cewar jaddada akidar kawo karshen irin wadannan hare-hare ba za su yi maganin komai ba, don haka ya zama wajibi shugabanni a Jamus su kare rayukan Musulmi da Yahudawa daga masu kyamar baki da suke kai hari.