An bukaci Özil ya bar buga wa Jamus wasa | Labarai | DW | 08.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci Özil ya bar buga wa Jamus wasa

Mustafa Özil mahaifin Mesut Özil shahararren dan wasan kwallon kafar nan na kasar Jamus ya bayyana bukatar ganin dansa ya dakatar da buga wa kungiyar kwallon kafar Jamus wasa a nan gaba.

Mahaifin Mesut Özil shahararren dan wasan kwallon kafar nan na kasar Jamus ya bayyana bukatar ganin dansa ya dakatar da buga wa kungiyar kwallon kafar kasar Jamus wasa a nan gaba, yana mai cewa an dora wa dan nasa karan tsana tun bayan da tun a zagayen farko aka fitar da Jamus daga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya. 

A wata hira da ya yi da jaridar kasar ta Jamus ta Bild Am Sonntag da aka wallafa a wannan Lahadi, Mustafa Özil mahaifin na Mezut Özil ya bayyana cewa mutane sun dora alhakin korar Jamus da wuri daga gasar kan dansa Özil wanda ya ce a yanzu jama'a na yi masa ihu suna zaginsa idan ya fito a bainar jama'a. 

Dama dai tun kafin a soma gasar ta cin kofin duniya Mesut Özil wanda dan asalin kasar Turkiya ne ya sha suka daga 'yan kasar ta Jamus da dama a sakamakon wani hoto da ya dauka tare da Shugaban Turkiyar Recep Tayyip Erdogan, abin da wasu Jamusawan suke ganin bai dace ba. 

Shima dai shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Jamus Reinhard Grindel ya yi kira ga dan wasan da ya fito ya yi wa jama'a bayani dalilansa na daukar wannan hoto da Shugaba Erdogan.