An ba wa sojojin Hungary karin ikon tinkarar batun ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 21.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ba wa sojojin Hungary karin ikon tinkarar batun 'yan gudun hijira

Wannan matakin da Hungary ta dauka ya zo daidai lokacin da kasashen Turai ke laluben hanyoyin magance matsalar ta 'yan gudun hijira da ke ci gaba da kwararowa Turai.

Kasar Hungary ta ba wa sojojinta karin iko a wani matakin shawo kan matsalar kwararar bakin haure. Wannan dai na zuwa ne gabanin wasu tarukan da kungiyar EU za ta yi a wannan mako kan yadda za ta tinkari tuttudowar 'yan gudun hijira zuwa Turai. A wannan Litinin 'yan majalisar dokokin kasar ta Hungary sun amince da matakin karshe na sabbin dokokin yaki da bakin haure. Karkashin dokokin an yarda sojoji su shiga cikin aikin tsaron kan iyakokin kasar sannan suna iya yin amfani da karfi, sannan su kuma 'yan sanda na da hurumin shiga gidajen jama'a don zakulo bakin haure. Firaminista Viktor Orban ya fada wa wakilan majalisar a birnin Budapest cewa baki na son su mamaye nahiyar Turai. Dubban daruruwan mutane da ke tsere wa yake-yake da kuma talauci suka shiga kasashen Turai a wannan shekara.