Aminu Tambuwal ya zama sabon kakakin majalisar wakilan Najeriya | Siyasa | DW | 06.06.2011
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Aminu Tambuwal ya zama sabon kakakin majalisar wakilan Najeriya

Bayan kai ruwa rana 'yan majalisar dokokin Najeriya sun kaɗa ƙuri'ar amincewa Hon Aminu Waziri Tambuwal a matsayin sabon kakakin majalisar inda ya doke abokiyar hamaiyarsa Mulikat Adeola.

Majalisar dokoki ta ƙasa a Najeriya

Majalisar dokoki ta ƙasa a Najeriya

A yau majalisar wakilai ta ƙasa a Najeriya ta zaɓi sabon kakakinta. Wanda aka zaɓa ɗin kuwa shine Alhaji Aminu Waziri Tambuwal na Jam'iyar PDP wanda ke wakiltar mazaɓar Kebbi da Tambuwal a majalisar tarayyar.

Tambuwal ya sami ƙuri'u 252 inda ya doke abokiyar takararsa Mulikat Adeola-Akande wadda ta sami ƙuri'u 90.

Tun da farko an sami rarrabuwar kawuna a tsakanin 'ya'yan majalisar game da batun shiyyar da zai fitar da kakakin majalisar.

Mukilat Adeola ta sami goyon bayan uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa wadda ta zaɓeta bisa tafarkin shiyya inda Jam'iyyar ta amincewa yankin kudu maso yamma ya fidda kakakin majalisar wakilan.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Karin shafuna a WWW

Sauti da bidiyo akan labarin