An haifi Aminu Waziri Tambuwa a shekarar 1966. A cikin shekarar 2015 ce aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.
Gabannin hawansa kan kujerar gwamnan Sokoto, Aminu Waziri ya kasance kakakin majalisar wakilan Najeriya a zamanin shugaban kasa na wancan lokacin Goodluck Jonathan.