1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun saci mutum sama da 50 a Sokoto

June 12, 2022

Shugaban karamar hukumar Tureta, inda aka kwashi mutanen, Abubakar Salihu, ya shaida wa DW cewa ''na fada wa sojoji lokacin da ake kai harin amma ba su je ba.''

https://p.dw.com/p/4CazU
Nigeria Parlamentspräsident Aminu Tambuwal
Hoto: picture alliance/Photoshot

A Najeriya, sama da mutane 50 ne 'yan bindiga suka kwasa a tsakanin jihohin Sokoto da Zamfara. Bayanan da DW ta tattaro na nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da yammaci, a lokacin da mutanen 'yan jihar Zamfara ke kokarin komawa gida Gusau bayan halartar wani daurin aure a garin Tambuwal. 

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun yi nasarar kwasar mutanen a tsakanin karamar hukumar Tureta da ke jihar Sokoto da Bakura da ke jihar Zamfara. To sai dai rahotanni na cewa wasu daga cikin mutanen da 'yan bindigar suka kwasa sun kubuta daga hannun maharan da suka addabi jihohin arewa maso yammacin Najeriya.