1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alƙaluma na wucin gadi a game da zaɓen ƙasar Nijar

February 3, 2011

Dangane da alƙaluma na wucin gadi da aka bayar game da zaɓen ƙasar Nijar, masana na hasashen cewar mai Mahamadou Isoufou da Seini Oumarou ne zasu shiga zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa.

https://p.dw.com/p/10AMW
Masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen NijarHoto: DW

A ci gaba da ƙididdigar ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa da majalisar dokokin da aka gudanar a ƙasar Nijar a farkon wannan makon, alƙaluman da hukumar zaɓe ta ƙasar ta bayar kawo yanzun dai sun nuna cewar Mouhamadou Isoufou shi ne ke kan gaba, sai Seini Oumarou dake bi masa a matsayi na biyu kana Hamma Amadou a matsayi na uku sai kuma Mahamman Usman dake biye musu a matsayi na huɗu. To ko wane irin martani ne aka fara mayarwa akan waɗannan alƙaluma? Ana iya sauraron rahoton da wakilinmu Mamman Kanta ya aiko mana daga birnin Yamai da kuma hira da ma'aikaciyarmu Pinaɗo Abdu ta gudanar da Farfesa Ado Mouhamman daga jami'ar Yamai, a can ƙasa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala