1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Tarayyar Turai: Karin tallafi ga Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 17, 2023

Al'ummar kasar Siriya da bala'in mummunar girgizar kasa ya rutsa da su, na ci gaba da samun kayan tallafi daga kungiyar Tarayyar Turai EU.

https://p.dw.com/p/4Nffu
Siriya | Tallafi | EU | Tarayar Turai | Girgizar Kasa | Yaki |
Dubban mutane ne bala'in girgizar kasa ya shafa a SiriyaHoto: FIRAS MAKDESI/REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai EU din ta bayyana cewa  kayan agajin da za su isa Siriyan, sun hadar da barguna da tantuna da kayan kicin da na'urar dumama daki da kuma kayan tsabtace wurare. Kayan dai za su fara isa  birnin Adana na Turkiyya ne, kafin kungiyar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Kasa da Kasa IOM ta mika su zuwa Arewa maso Yammacin Siriyan da ibtila'in girgizar kasar ya shafa. Tuni dai wasu jiragen dauke da kayan agaji suka isa birnin Beirut na kasar Lebanon domin tallafawa Siriyan.